(ABNA24.com) Kakakin kungiyar Taliban ne, Suhail Shaheen, ya sanar da hakan ga kamfanin dilancin labaren AFP, saidai bai fayyace ko wadanne bangarori zasu halarci taron ba.
Amma a cewarsa tawagar kungiyar zata isa a birnin na Pekin a ranakun 19 da 30 ga watan Oktoba nan.
An dai cimma wannan matsaya ce bayan wata ganawa a Doha, tsakanin shugaban ofishin siyasa na kungiyar ta Talibanda kuma wakilin musamman na kasar China, Deng Xijon.
Saidai kawo yanzu babu wani bayyani daga gwamnatin ta Afganistan kan taron.
........
340